A Real Madrid Nake So Na Yi Ritaya – Luka Modric

Luka Modric a tsakiya suna murnar zura kwallo a gasar Champions League tare da Vazquez da Vinicius

“Ina fatan ci gaba da zama anan har zuwa wasu karin shekaru masu zuwa sannan na kammala rayuwarta ta kwallo a nan.” Modric wanda dan asalin kasar Croatia ne ya ce.

Dan wasan Real Madrid Luka Modric ya ce yana fatan a kungiyar zai kammala rayuwarsa ta kwallo.

Modric ya bayyana hakan ne a lokacin da ya shiga jerin gwarazan ‘yan wasan motsa jiki na duniya da aka yi na bikin “Marca Legend Award” a ranar Laraba, kamar yadda AP ya ruwaito.

Fitattun ‘yan wasan motsa jiki na duniya irinsu Michael Jordan, Lionel Messi, Muhammad Ali, Cristiano Ronaldo, Fernando Alonso, Rafael Nadal, Ronaldo Nazario, Pele, Niki Lauda da Johan Cruyff da sauransu, sun samu wannan kambu.

Dan shekara 36, dan wasan tsakiyar na Real Madrid ya taka muhimmiyar rawa a wannan kakar wasa, wacce ta taimakawa kungiyar ta lashe kofin La Liga na Sifaniya.

Kungiyar har ila yau ta kai wasan karshe na Zakarun Nahiyar Turai, wato Champions League inda za ta kara da Liverpool a karshen watan nan na Mayu.

“Real Madrid gida ne a wuri na. Na kasance mai cike da farin ciki a wannan kungiya da birni, na kan kuma ga irin soyayya da magoya suke nuna min. Iyalina suna jin dadin zama a nan.

“Ina fatan ci gaba da zama anan har zuwa wasu karin shekaru masu zuwa sannan na kammala rayuwarta ta kwallo a nan.” Modric wanda dan asalin kasar Croatia ne ya ce.