A Nijar Wata Kotun Kasar ta Saki Wasu 'Yan Jarida da Dankuiyar Farin Kaya da Hukumomin Kasar Suka Tsare.

Mr. Morou Amadou ministan shari'a na Nijar.

Rahotanni daga Nijar suna nunin cewa an saki wasu 'yan jarida biyu da kungiyar farin kaya da 'yan sanda suka tsare tun ranar litinin.
A wunin Alhamis dinnan ne wata kotun a Nijar ta saki wasu 'Yan jarida biyu da dan kungiyar farar hula da jami'an 'Yansanda suka rike dasu tun ranar litinin d a ta wuce sakamakon zargin su da hukumomi suke yi cewa sun yi kalaman batunci ga mahukunatan kasar a kafofin yada labarai masu zaman kansu.

Wannan sakin ya zo ne 'yan kwanaki da sakin wasu 'yan jarida biyu da gwamnatin ta kama a baya bayannan ciki harda wakilin mu Abdoulaye Mammane Ahamdou.

Abdoulaye Mammane Ahmadou ya zanta da shugaban kungiyar masu kafofin yada labarai masu zaman kansu a Nijar, Mallam Shu'aibu Mamane, inda yace suna tur da Allah wadai da wannan kame kamen da ake yiwa manema labarai.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kama 'Yan Jarida a Nijar