Mutanen Junhuriyar Nijer sunce gwamnati na yi musu ijoro gameda kulla sabuwar yarjejeniya da kampanin Areva
WASHINGTON, DC —
Wata tawagar kanfanin Areva mai kwantaragin hako karfen uranium a Nijer ta kawo karshen wata ziyarar aiki ta kwanakki 2 a Nijer da zummar sake tattaunawa da mahukuntan kasar kan sake wata yarjejeniya hako karfen uranium. Sai dai kuma wasu kungiyoyin fararen hulla sunyi tir da Allah wadarai da kokarin kulla sabuwar yarjejeniyar ba tare da shedawa ‘yan kasar ta Nijer ba, kamar yanda kundin tsarin mulkin kasar ya shardanta. Daga Niamey ga Rahoton Abdoulaye Mamane Amadou: