A Niger Likitoci Suna Fadakar Da Mata Muhimmancin Shayar Da Nonon Uwa.

UNICEF logo

A jamhuriyar Niger likitoci na ci gaba da wayar da kawunan al’umma a alabarkacin mako na musamman da aka ware a duniya domin fadakarawa akan mahimancin shayar da jarirai nonon uwa da kuma illar da rashin hakan ke haifarwa uwa da danta.

Masana sun sanar cewa shayar da jarirai nonon uwa zalla daga ranar haifuwa zuwa watanni 6 a duniya, wata hanya ce dake kare yara daga kamuwa da cututtuka. Saboda haka ne hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, suka ware kwanaki 7 a farkon watan Agustan kowace shekara, domin fadakarwa kamar yadda shugaban asibitin haifuwa dake Yamai Dr. Mamman Sani ya bayyana.

Rashin mutunta tsarin shayar da jarirai nonon uwa zalla har zuwa watanni 6 na farkon rayuwarsa, wani babban kuskure ne da likitoci suka tabbatarda cewa yana jefa yaro cikin hadari. Saboda haka Dr. Mamman Sani, ya gargadi iyaye su dukufa wajen shayar da jariransu da nononsu har yaro ya kai akalla wata 6 ka fin su fara hadawa da abinci. Yin hakan, zai gina wa yaro rigakafin wasu cututuka tare da gina jikinsa domin ya rayu sosa.

Asusun tallafawa yara na MDD ko UNICEF a takaice, ya bayyana cewa yara 3 daga cikin 5 ne a duniya aka gano cewa ba sa samun sukunin shan nonon uwa zalla har zuwa watanni 6 na farkon zuwansu doron kasa, sanadiyar wasu dalilai da ake dangantawa da ala’adun Afirka, inda dangin mai jego kan dauke yaro dagayi hanun mahaifiyarsa alokacin da ake bukatar yana shan nonon uwar.

​A saurari rahoton Souley Barma domin karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

A Niger Likitoci Sun Fadakar Da Mata Mahimmancin Shayar Da Jarirai Nonon Uwa - 2' 52"