Tun daga farkon wannan shekarar, sau biyu likitocin dake aikin kwantiragi suka yi yajin aiki bisa umurnin kungiyarsu saboda rashin samun albashi.
Likitocin sun kwashe watanni bakwai ba tareda samun ko kwandala ba daga gwamnati a matsayin albashi duk da cewa watan jiya gwamnati ta yi alkawarin rage bashin albashin dake kanta.
Malama Rabi Muhmmadu wata likita ‘yar kwantiragi dake aiki a karkara ta ce har yanzu ba’a biya su ba. Tace tun da aka biya su albashin wata guda ba’a kara waiwayansu ba. An sa su cike wasu takardu amma yar yanzu basu ji komai daga hukumomi ba.
A wata hira da ya yi da Muryar Amurka a watan jiya dangane da matasalolin likitocin, ministan kiwon lafiya na kasar Dr Iliyasu Iddi Mainasara yace gwamnati na duba hanyoyin kawo karshen matsalar. Y ace yanzu za’a kirkiro hanyar biyansu saboda gwamnati ta amince da ayyukan da suke yi.
Lamarin da likitocin karkara ke ciki ya sa wasu cikinsu soma ajiye aiki da nufin neman wata madogarar ta daban.
Saurari rahoton Souley Barma domin jin karin bayani
Facebook Forum