Matsalar karancin mai na jiragen sama masu jigilar fasinja ya fara jawo cikas a zirga zirgar jiragen sama a Najeriya.
Daya daga cikin darektocin jiragen fasinja na kamfanin Arika Najeriya keftin Ado Sanusi, yace tilas ne a fuskanci wannan mtsala ganin mutum daya ne kawai yale da izinin shigo da mai da jiragen suke amfani da shi daga kasashen waje.
Ana sa bangaren wani jami'in kamfanin jigilar fasinja yace muddin ana son a sami saukin wannan lamari to tilas gwamnati ta kyale wasu karin mutane su shiga kasuwancin shigo da mai da jiragen saman suke amfani da shi.
A gefe daya kuma gwamnatin jihar Benin ta rufe tashar jiragen sama dake jihar tana zargin cewa gwamnati bata biya jihar kudaden haraji da suka kamata a biyata. Ga Ladan Ibrahim Ayawa da rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5