Masu Zanga-zangar sun hallara a dandalin wasa na Liberation Stadium da ke birnin Fatakwal don yin wannan zanga-zangar. To saidai ba su iya maci ba kamar yadda su ka so saboda 'yan sanda sun tarwatsa su saboda wai ba su bi ka'idar yin zanga-zanga ba kuma akwai dokar hana yin zanga-zanga. Jami'ar hulda da Jama'a na Rundunar 'Yan sandan jihar Rivers Mrs Angela Agabi ta gaya wa wakilinmu na yankin Naija-Delta, Lamido Abubakar cewa 'yan sandan sun tarwatsa masu zanga-zangar ne saboda sun nuna taurin kai ta yadda ko takardar neman izinin yin zanga-zangar ba su rubuta wa 'yan sanda ba.
Wani dan asalin jihar ta Rivers mai suna Tamuno Tabo ya gaya wa wakilinmu cewa akasarinsu ba su tare da Gwamna Amaechi saboda ba ya girmama na gaba da shi. Don haka, a cewarsa, batun yin zanga-zanga ma ai bai taso ba. To amma wani dan jam'iyyar PDP ta su Gwamna Amaechi din mai suna Alhaji Ali Kwande ya ce rikincin tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan da Gwamna Amaechi a yanzu ya zarce rikicin mutanen biyu; ya zama rikicin 'yan Nijeriya, kuma akwai fargabar ma rikicin zai wanzu.