Da ya ke bayani ga wakilinmu na jihar Borno Haruna Dauda Biu, bayan ganawa da wata tawagar Kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya kan Batun Tsaro da ke ziyara a jihar, Mataimakin Gwamnan jihar ta Borno Alhaji Zannan Umar Mustapha ya ce ba shakka wayar salula na taimakawa wajen kai hare-haren da ake yi a jihar, kuma sun ga fa'idar katse wayar. Ya ce jihar Borno ce ta fi fama da munanan hare-haren da aka yi ta kaiwa, don haka sun gwammace rashin aiki da wayar salula da rashin kwanciyar hankalin da wayar ke janyo masu.
Kwamitin Majalisar Dattawan ya kai ziyara jihar ta Borno ce don gane wa kansa cigaban da aka samu ko akasin haka da kuma irin korafi ko shawarar da jama'a da hukumomin da abin ya shafa ka bayar.