A Myanmar An Ruguza Gidajen Yan Kabilar Rohingya Sama Da Dubu

Burma

Kungiyar nan mai kare hakkin bil adama ta Huma Rights Watch, ta ce ta na da hujja da ta samu ta tauraron dan adam, dake nuna cewa an rusa fiye da gidaje dubu daya mallakar ‘yan kabilar Rohingya a Arewa maso yammacin Myanmar ko kuma kasar Burma.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnati da ta gayyaci Majalisar Dinkin Duniya, domin a gudanar da bincike kan rusa gidajen yankin, wanda ake zargin dakarun gwamnatin kasar ne suka yi.

Darketan kungiyar a yankin Asiya, Brad Adams, hotunan tauraron dan adam, sun nuna cewa ta’asar da aka aikata wajen rusa gidajen tafi yadda gwamnati ta kwatanta lamarin nesa ba kusa ba.

Adams ya kuma kara yin kira ga gwamnatin ta Myanmar, musamman ga Aung San Suu Kyi, mai lambar yabo ta zaman lafiya, da su dena mai da martani da amfani da tsarin karfin soji da aka gani a baya, a maimakon haka a rika baiwa kowane mutum kariya, ba tare da la’akkari da kabila ko addinin mutum ba.

Kungiyoyi masu ayyukan jin kai sun ce, dubban mutane ne suka rasa muhallansu sanadiyar wannan rikici, lamarin da ya sa da yawnasu suka tsere zuwa Bangladesh.