Shugaban kasar ta Japan, wanda shine shugaban wata kasar waje na farko da ya gana da Trump, yana wannan kalamin ne bayan haduwar da suka yi jiya a katafaren gidan nan mai soraye da yawa na shi Trump din dake birnin New York.
Sai dai Mr. Abe bai bada wani karin haske kan abubuwan da suka tattauan ba, haka shima Trump din ya kama bakinsa ya tsuke, bai ce komai ba bayan taron nasu.
A lokacinda yake yakin neman zabe, Donald Trump ya sha sukar lamirin dangatakar dake tsakanin Japan da Amurka inda ya nuna cewa Amurka tana kashe mankudan kudade wajen tsaron kasar ta japan.
A wancan lokacin har ma Trump ya kawo shawarar a bar Japan da wasu kasashe na yankin kowaccensu ta sami makaman kare dangi na nukiliya, kuma a tilasta musu su rinka biyan Amurka mankudan kudade in suna son ta rinka aika sojanta zuwa kasashensu.
Yanzu haka dai Amurka na da sojoji kamar 53,000 a can Japan wadanda ke tare da iyalinsu da aka ce sun kai 43,000 da kuma ma’aikatan fararen hula kamar 5,000.