Wata dokar Rome ce dai ta kafa wannan kotun a shekarar 1998. Putin ya sanya hannu a kan yarjejejniyar amincewa da kotun shekarar 2000 amma Rasha bata tabattar da hallacinta ba.
Wata mace da ake kira Tanya Lokshina, ‘yar kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch dake a birnin Moscow ta fada a wani sakonta na email cewa ficewar Rasha daga kotun ICC wata alama ce dake nuna yanda Rasha bata mutunta hadin kai ga shari’ar kasa da kasa da kuma hukumomin tabattarda adalaci na kasashen duniya.
Lokshina tace sanya hannun da Rasha ta yi akan wannan dokar kafa kotun tun shekara da shekaru, na nuna amincewarta da kuma yin aiki da kotun.
Yanzu kuma Rasha ta fito karara tana cewa bata son abin da kotun ke yi kuma tayi watsi da tsarin shari’a kasa da kasa.
Wannan matakin ficewa daga kotun ta duniya da Rasha tayi dai ya faru ne kwana daya bayanda wani rahoto na kotun ya la’anci mamayen da rasha din tayi wa yankin crimea na kasar Ukraine.