A Milwaukee An Kafawa Yara Dokar Hana Fita Daga Karfe 10 Na Dare

Masu Zanga Zanga

Jami'ai a birnin Milwaukee da ke yankin yamma ta tsakiya a jahar Wisconsin sun kafa ma yara masu kuruciya dokar hana yawo tun daga karfe 10 na dare sanadiyyar dare biyu da aka shafe ana ta bore, bayan da 'yan sanda su ka harbe wani bakar fata ranar Asabar.

"Ya iyaye, bayan karfe 10, yaranku masu kuruciya su fa kasance a gida, ko kuma wani wurin da ba kan titi ba," a cewar Magajin Gari Tom barrett a wani taron manema labarai da ya kira jiya Litini. Ya kuma ce jami'an sun tattauna da attoni-janar na birnin don shirin yiwuwar a yanke shawarar fadada dokar hana fitar.

Barrett ya yi wannan sanarwar ce yayin da ake cigaba da zaman dardar kuma 'yan sanda sun daura damara, yayin da kuma dogarawan tsaron kasa ke shirye, ko a tura su muddan bukatar hakan ta taso.

Rundunar 'yan sandan Milwaukee ta ce an harbe wani dan shekaru 18 da haihuwa yayin zanga-zanga ranar Lahadi kuma an yi amfani da mota mai sulke wajen kai shi asibiti. To amma ba a samu rahoton irin barnace-barnacen da aka gani ranar Asabar ba, lokacin da aka kona wuraren kasuwanci akalla 6.