A Juma’ar da ta gabata, NLC ta ayyana zanga-zangar kwanaki 2 a fadin kasar nan akan halin matsin da ‘yan Najeriya ke fuskanta da kuma matsalar tabarbarewar harkokin tsaro a fadin kasar.
Sai dai a wata sanarwa da me magana da yawunta, Peter Afunanya ya fitar, DSS ta bukaci bangaren ‘yan kwadagon ya bi tafarkin tattaunawa a maimakon hanyoyin daka iya kara yamutsa hazo.
Sanarwar ta kara da cewar gwamnatoci a dukkanin matakai na iya bakin kokarinsu wajen rage radadin halin kuncin da ake ciki, don haka ya kamata a kyautata musu zato.
An ruwaito wani sashe na sanarwar na cewar, an ja hankalin hukumar tsaro ta dss ga wani shiri da hadaddiyar kungiyar kwadago na gudanar da zanga-zanga a tsakanin ranaikun 27 da 28 na watan Fabrairun da muke ciki a wasu sassan Najeriya game da tabarbarewar tattalin arziki da wasu batutuwa.”
“Duk da cewar hukumar DSS ta amince da cewar gudanar da zanga-zangar hakkin da kundin tsarin mulkin kasa ya halastawa kungiyar kwadagon, saidai muna kira dasu jingine wannan shiri da ci gaba da wanzuwar zaman lafiya da walwalar jama’a.”
“DSS ta kuma yi kira ga kungiyoyin kwadagon dasu bi tattauna da gwamnati a maimakon yin al’amuran daka iya kara yamutsa hazo. Musammanma da DSS ta fahimce cewar wasu batagari na shirin amfani da damar zanga-zangar wajen haddasa rikici daka iya mamaye kasar. Ko shakka babu, hakan na iya kara ta’azzara halin matsin rayuwar da ake fama da shi a fadin Najeriya.”