WASHINGTON D.C —
A Rasha hukumomin kasar jiya lahadi, suka fara gudanar da bincike bisa zargin an aikata laifi, sa'o'i bayanda yara akalla 14 da suke halartar wasu shirye shiryen bazara na matasa a arewa maso gabashin kasar suka mutu, lokacinda kananan jiragen ruwa da suke ciki suka kife yayin da ake ruwan sama a wani tabki kusa da kan iyaka da kasar Findland.
Da yake magana jiya Lahadi, kakakin hukumar bincike na kasar, yace yara 47 da manya hudu wadanda suke musu jagora da horaswa ne suke cikin kananan jiragen ruwa hudu lokacinda bala'in ya auku.
Haka nan yace an tsare mutane hudu wadanda suke aiki a sansanin da aka shirya domin matasan saboda a yi musu tambayoyi, da wasu manya biyu, wadanda ake zargi sune suka shirya balaguro cikin ruwan.