Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Samari? Duk Maccen Da Ta Cika Kyau, To A Gujeta!


Sinadaran Gyaran Fata!
Sinadaran Gyaran Fata!

Daga neman kiba ana iya samo rama, idan ba’ayi hattara ba. ‘Yan mata da kanyi abu don burge ko neman samari, sai ayi hattara. Wani bincike da aka gudanar da ya bayyanar da mafi akasarin ‘yan mata a wannan zamanin, su kanyi amfani da wasu kayan shafe-shafe da suke shafa ma fuskokin su da jikin su, batare da sanin wadannen sinadarai akayi amfani da su wajen hada abubuwan ba.

Binciken ya bayyanar da yadda kayan shafe-shafen ke nakasar da fatar jiki, da kuma sama fata cutar kansar fata. A cewar wani shahararren likitan fata a asibitin fata da wasu kananan cuttutuka na garin Saye a birnin Zaria. Dr. Mahmmud Abdullahi, yace wadannan sinadaran suna da matukar illiga ga lafiya duk wata mace da take amfani da su.

Domin kuwa idan mace na yawan amfani dasu, kuma bata kokarin wanke fuskarta da kyau don gudun kada kwalliyar ta gudu, to babu shakka za’a kai lokacin da kwayoyin dake kare fatar zasu daina aiki yadda ya kamata. Daga nan sai kowace cuta zata samu damar shiga, don babu wani abu da zai hanata shiga, ko kuma ya fitar da ita. Don haka akwai bukatar ‘yan mata su kula da irin kayan shafe-shafen su da kokarta gyaran jiki yadda ya kamata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG