A Kasar Kamaru Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Sarkin Balondo

Wasu cikin sarakunan gargajiyan kasar Kamaru

Bisa zargin da kabilun sashen dake anfani da harshen Ingilishi ke yi na cewa sarakunansu na hada baki da gwamnati, yanzu sun soma bin sarakunan suna kashesu daya bayan daya

Wasu shugabannin kabilu da ke sashin Ingilishi a yankin kudu maso yammacin Kamaru, sun tsere daga fada bayan da wasu 'yan bindiga su ka fitar da sarkin Balondo daga cikin wani coci karfi da yaji su ka kashe shi. 'Yan awaren yankin sun kama tare kuma da kashe wasu sarakunan yankin saboda wai suna zarginsu da laifin hada baki da gwamnati.

Tawaye da tashe-tashen hankula sun barke a sashin Ingilishi na yankin Kudu maso yammaci da kuma kudu maso kudncin kasar ta Kamaru a karshen shekarar 2016, saboda tilasta amfani da harshen Faransanci da aka yi a makarantu da kotuna da sauran cibiyoyin gwamnati a lokacin. Kungiyoyin 'yan tawaye na gwagwarmayar neman 'yancin kan kasarsu da su ke son su kira ta Ambazonia.

Sarki Itoh shi ne sarki na takwas da 'yan bindiga su ka hallaka a yankin na kudu maso yammacin kasar cikin watannin hudu da su ka gabata.