Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kamaru Ta Tsare Sojoji 7 Da Ake Zargi Da Kashe Mata Da Yara


 Paul Biya, shugaban kasar Kamaru
Paul Biya, shugaban kasar Kamaru

An tsare sojoji 7 ne da ake zargi da kashe mata da yara yayinda suke fafatawa da kungiyar Boko Haram a shekarar 2016, lamarin da ya Amnesty International ta yabawa gwamnatin Kamaru

Mahukuntar kasar Camaroon sunce yanzu haka suna tsare da sojojin su 7 da ake tuhumar sun kashe mata da yara a shekarar 2016 lokacin da suke yaki da kungiyar Boko Haram.

Kungiyar kare hakin bil adama ta Amnesty International tace wannan matakin da gwamnati ta dauka yana kan hanya, tace sai dai akwai bukatar a kara zurfafa bincike akan wadannan kashe-kashen da sojojin kasar keyi.

Wakilin muryar Amurka daga Cameroon Moki Edwin Kindezeka ya aiko da rahoto daga Yaounde cewa kungiyar ta kare hakkin bil adama ta yaba da wannan matakin da gwamnatin ta Cameroon ta dauka na kame sojojin da ake tuhuma da kashe fararen hula lokacin da suke yaki da kungiyar boko haram.

Mai Magana da yawun gwamnatin kasar ta Cameroon Isah Tchiroma yace sojojin nan 7 an kama su ne a cikin satin data gabata, a saboda kashe mata biyu da yara biyu da suke zargi da laifin goyon bayan kungiyar boko haram.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG