Jiya Laraba wata karamar yarinya ‘yar kunar bakin wake ta fasa nakiyoyin dake jinkinta a cikin wani Masallacin kasar Kamaru, inda kuma har mutane akalla biyar suka rasa rayukkansu.
Gwamnan yankin da abin ya faru, Midjinyawa Bakery yace bayan kiran sallar Asubah na farko ne yarinyar, mai kamar shekaru 12 ko 13 da haihuwa, ta shiga cikin masallacin inda ta yi ta’addancin.
Har zuwa yanzu dai ba wata kungiyar da ta dauki alhakkin wannan harin amma dai an san cewa kungiyar Boko Haram ta jima tana gudanar da yaki akan iyakokin kasashen Nigeria, Chad, Junhuriyar Nijer da kuma Kamaru.
A cikin makon jiya ne kungiyar kare hakkin Bil Adama ta “Amnesty International” ta fadi cewa mutane sama da 400 aka hallaka a Nigeria da Kamaru daga watan Afrilun wannan shekara zuwa yanzu, wanda ya ribanya yawan mutanen da aka kashe a cikin wannan lokacin a wattanin da suka gabata.
Facebook Forum