A Kasar Indonesia Ana Yiwa Wadanda Suka Karya Dokar Coronavirus Hukuncin Kaskanci

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasar Indonesia na lura da abin da suka bayyana azabar kaskanci da ake yiwa mutanen da suka ki bin dokar da aka saka don yaki da cutar coronavirus da saka tukunkumin fuska.

Hukuncin ba abin da aka saba gani bane, da suka hada da tilastawa wadanda suka karya dokar shiga cikin makara su zauna ko kuma su ha’ka kabari, a cewar kungiyar kare hakkin bil Adama ta (KontraS).

Kungiyar ta samu hukunci masu kankanci har 10 da aka yiwa mutane tun lokacin da aka saka dokar kulle a watan Afrilu a wasu yankuna na Indonesia. Kasar ita tafi yawan samun mutanen da suka mutu daga coronavirus a kudancin yankin Asia, inda sama da mutuum 10,300 suka mutu, kamar yadda bayanan cibiyar binciken coronavirus ta jami’ar Johns Hopkins suka nuna.

Indonesia ta samu mutum 271,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar dake da yawan mutane miliyan 270.6, a cewar bankin duniya.

Rivanlee Anandar, dake zaman mamba a kungiyar KontraS, ya fadawa Muryar Amurka cewa hukuncin na kaskanci da ake yiwa mutane wanda hukumomi yankuna ke suka saka, ciki har da tilastawa mutane kwanciya kusa da makara, yayin da ake amfani da ‘yan sandan kasar da sojoji suna kula da hukuncin.

Evani Jesselyn, wadda take da shagon sayar da shayi a Jakarta, an fada mata cewa za ta wanke bututun da kashin al’umma ke wucewa ko ta biya tara, bayan da aka tsare ta tana tafiya cikin motarta ba tare da ta saka takunkumi ba.