Bernard Lawes dan shekaru 87 ya shafe shekaru70 bai ga likita ba sabili da yana cikin koshin lafiya, bai kuma taba fasa zuwa aiki ba ko da na kwana daya sabili da rashin lafiya tunda ya fara aiki har ya yi ritaya.
Bernard ya bayyana cewa, ya je ganin likita na karshe a shekarar 1950, yana da shekara 18, da haihuwa lokacin da aka je ayi mashi gwaji kafin ya tafi bautar kasa.
Bernard ya bayyana cewa, sirrinshi shine cin abinci mai zafi a kalla sau daya a rana, da kuma taka da’ira. Ya kuma ce bai taba shan giya ko taba ba a rayuwarsa.
Benard yana hawan bene mai matakala 110 sau uku a mako domin ya je ya wana agogon majami’arsu, kuma ya yi wannan aikin sa kai na tsawon shekaru 44, inda ya tafiya kan matakala 750,000 a tsawon shekarun nan.
Kafin ya yi ritaya yana mai shekaru 60, yana takawa domin motsa jiki na tsawon mil hudu domin kara samun lafiya da karfin jiki.
Benard wanda bai taba mallakar mota ba. yace yana iya takawa ya je neman dukan abinda na ke bukata, yace mutane ba su taba yarda idan ya gaya masu cewa bai je ganin likita ba cikin shekaru 70. Ya kuma bayyana cewa motsa jiki yana da muhimmanci ainun, ba bu wani sirri sai dai kawai motsa jiki da kuma cin abinci da ya dace. Ya kuma ce cudanya da jama’a yana da amfani.
Benard wanda ya bayyana cewa ya yi wasanni kamar kwallon kafa da kwallon raga, yana kuma jin dadin aikin lambu, abinda yace ya fi daukar hankalinsa yanzu da ake rage cudanya da jama’a sabili da annobar Coronavirus
Facebook Forum