Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Mutuwa Sanadiyyar COVID-19 Zai Iya Kai wa Miliyan Biyu - WHO


Shugaban hukumar WHO, Adhanom Ghebreyesus a birnin Geneva Switzerland, ranar 3 ga watan Yuli, 2020.
Shugaban hukumar WHO, Adhanom Ghebreyesus a birnin Geneva Switzerland, ranar 3 ga watan Yuli, 2020.

Wani jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar adadin wadanda ke mutuwa sanadiyyar annonar COVID-19 a duniya ya kai miliyan biyu idan har ba a samu ingantacciyar allurar rigakafin cutar ba.

Jami’in ba da kulawar gaggawa a hukumar, Dr Mike Ryan, ya ce adadin zai iya hauhawa idan kasashen duniya ba su rungumi wani tsari kan yadda za a dakile yaduwar cutar ta coronavirus ba.

Yanzu haka cutar ta yi sanadin mutuwar kusan mutum miliyan daya a duk fadin duniya sannan ta harbi mutum miliyan 32.5 a cewar alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta fitar.

Gargadin jami’in na hukumar Lafiya ta duniya WHO na zuwa ne, yayin da nahiyar turai ke ganin barkewar cutar a karo na biyu, lamarin da ya sa gwamnatoci a sassan nahiyar suka maido da matakan hana yaduwar cutar.

Firai Ministan kasar Netherland, Mark Rutte ya bayyana hauhawan adadin masu kamuwa da cutar a matsayin “babban abin damuwa, yayin da kasar take ba da rahoton samun sabbin masu kamuwa da ita, wadanda adadinsu ya kai 2,777 a rana guda.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG