A Karon Farko cikin Shekaru Shida Gwamnan Borno Ya Ziyarci Gwoza

Gwamnan Borno Kashim Shettima

Bayan yayi mako daya a garin Bama gwamnan jihar Borno ya kai ziyara karamar hukumar Gwoza inda ya kai masu tallafin kayan abinci tare da yi masu alkawarin shafemasu hawayensu

Gwamnan ya fara yada zango ne a garin Pulka daya daga cikin garuruwan da 'yan Boko Haram suka mamaye a can baya.

Gwamnan da tawagarsa sun ga abubuwa masu ban al'ajabi da dama tunda suka taso daga Bama zuwa garin Gwoza. Sun ga ramuka da dama akan titi sanadiyar bamabamai da yan ta'adan suka binne.Ramukan basu da adadi.

Mazauna garin sun bayyana damuwarsu. Suna fama da rashin abinci da rashin ruwan sha. Lokacin rikicin yawancin mutanen garin gudu suka yi wasu kuma an kashesu.

Mutanen garin basa iya fita bayan garin sosai saboda haka basa zuwa gonakansu dake can bayan gari sai dai su yi shuka kusa kusa saboda har yanzu 'yan Boko Haram sukan kashe mutane a bayan gari.

Yayinda gwamnan yake magana dasu yayi masu alkawarin taimaka masu da zara ya koma Maiduguri. Zai taimaka su samu ruwan sha da kuma gyara hanyarsu. Amma gwamnan yana tafe da buhuwan abinci da sauran wasu kayan abinci domin tallafawa mutanen karamar hukumar.

Kayan abincin da gwamnan ya kai Gwoza

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Karon Farko cikin Shekaru Shida Gwamnan Borno Ya Ziyarci Gwoza - 3' 58"