A Karon Farko, Ana Shirin Mika Mulki Daga Gwamnatin Farar Hula Zuwa Wata a Nijar

Taron Jam'iyyar PJP a Nijar

Jamhuriyar Nijar ta dauki hanyar kafa tarihi, inda a karon farko zababbiyar gwammatin farar hula za ta mika mulki ga wata takwararta ta farar hula ba tare da wata tangarda ba.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, wanda ke shirin kammala wa’adin mulkinsa na shekara biyar-biyar sau biyu, zai sauka bayan wannan zabe da ake yi a zagaye na biyu.

Ana zaben ne tsakanin tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR Canji da abokin hamayyarsa tsohon ministan cikin gida, Bazoum Mohamed na jam’iyyar PDNS Tarayya mai mulki.

Wannan kuma shi ne zagaye na biyu, bayan da ‘yan takara 30 da suka kara a zagayen farko suka gaza samun kashi 50 na kuri’un da ake bukata kafin dan takara ya samu nasara.

Shi dai Bazoum ya samu kashi 39 da dan doriya yayin da Ousman ya samu kashi 17 shi ma da dan doriya.

Hakan ya ba ‘yan takara biyu damar zuwa wannan zagaye na biyu na ranar 21 ga watan Fabrairu.

Tandja Mamadou

Tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga kasar Faransa a shekarar 1960, Nijar ta sha fama da juyin mulkin soji lamarin da ya sa ba ta taba samu an mika mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata ba.

Juyin mulki na baya-bayan nan ya faru ne shekara goma da suka gabata inda aka hambarar da gwamnatin marigayi shugaba Tandja Mamadou a lokacin da ya yi yunkurin yi tazarce.

Yadda wannan zabe ya gudana shi ne zai tabbatar da ko kasar za ta kai ga gacin sauya mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata ta farar hula.

Gangamin yakin neman zaben da aka yi, bai nuna alamun za a samu wata tangarda ta tashin hankali ba, ko da yake an dan samu yanayi na jefa zafafan kalamai a nan da can a lokacin yakin neman zabe. Ita dai Nijar ba santa da matsalar tarzomar zabe ba.

Sannan babban abin da wasu ke ganin ya dora kasar a kan wannan turba ta mika mulki cikin lumana shi ne yadda shugaba mai barin gado Issoufou zai fice ba tare da ya nemi wa’adi na uku ba.

Hakan ya sa yake shan yabo a ciki da wajen kasar ta Nijar, duba da yadda a kwanan nan shugabannin Ivory Coast da Guinea suka yi tazarce duk da cewa sun kammala wa’adinsu biyu.

Ousmane ya kasance shugaban kasa na farko da aka zaba karkashin mulkin dimkoradiyya. Ya jagoranci kasar daga 1993 zuwa 1996, inda daga baya sojoji suka yi masa juyin mulki.

Bazoum tsohon ministan cikin gida ne ya kuma taba rike ministan harkokin waje shi ne kuma dan takarar da jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ta tsayar.

Babban kalubale biyu da ke fuskantar kasar ta Nijar wacce ba ta da iyaka da teku su ne, matsalar tsaro da kuma talauci.

‘Yan ta’addan kan iyakokin Mali da Boko Haram a Najeriya da Aljeriya, na daga cikin manyan batutuwa da ke haddasa matsalar tsaro a kasar ta Nijar.

Kwanaki bayan kammala zabe a zagayen farko, ‘yan bindida da ba a san ko su waye ba, sun kashe gwamman mutane a Gundumar Oualama da ke Nijar.