A Kano An Gudanar da Taron Horas da Jama'a Akan Tsaro

'Yansandan Najeriya.

Mutanen da aka horas dasu sun fito ne daga sassa daban daban na alamuran rayuwar yau da kullum a Kano.

Rundunar 'yansandan jihar Kano da hadin gwiwar wani kamfanin harkokin tsaro mai zaman kansa suka shirya taron domin zaburar da jama'a ta yin la'akari da kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a yanzu.

Shugaban kamfanin kuma daya daga cikin wadanda suka gabatar da mukala ga mahalarta taron yace bayan bayanai masu tarin yawa sun yi masu bayani akan idan ana harbe-harbe lokacin da mutum ke tafiya a kasa to sai ya kwanta a kasa domin mutum bai isa ya tserewa gudun bindiga ba. Komi yaya ta fi mutum gudu. Bayan mutum ya kwanta to sai ya cigaba da rarrafawa da jan ciki kana mutum ya gangara inda zai samu mafaka.

Inda ake kira mafaka zai zama kamar wurare biyar ko da fi. Daya a yi sauri a fada gwata, cikin ramin da ruwa ke kwarara. Na biyu ana iya buya bayan pol din waya. Idan kuma akwai dutse babba ana iya buya bayansa. Idan akwai gine-gine su ma abun buya ne.

Idan mutum ya ji bam ba'a gudu kwantawa a keyi domin hadarin zai ragu kwarai da gaske.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun ce ya kara masu kaimi da ilimi akan abun da suka sani dangane da harkar tsaro. Zasu fadakar da ma'akatansu da 'yanuwa da ma na kusa dasu. Taron ya jaddadawa jama'a cewa koina suke yakamata su yi taka tsantsan . Akwai matakan kare kai ba tare da dogara da jami'an tsaro ba.

Masana da jama'ar gari na ganin yakamata a cigaba da horas da mutane akan matakan da zasu dauka na tsaro domin kare kansu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Kano An Gudanar da Taron Horas da Jama'a Akan Tsaro - 3' 25"