A Jihar Neja 'Yansanda Sun Kwato Shanun Sata

Shanun sata da 'yansanda suka kwato

'Yansandan jihar Nejan Najeriya sun samu nasarar kwato wasu shanun sata masu dimbin yawa tare da cafke barayin shanun da makamansu

Rundunar 'yansandan jihar Neja ta samu kwato shanun sata guda 349 tare da kwato makamai daga hannun barayin shanun kimanin su 44.

Kakakin rundunar ASP Bala Elkana yace sun samu nasarar kwato shanun ne biyo bayan samamen da suka kai a lokuta daban daban a cikin dajin da barayin ke boyewa idan sun sato shanun.

Kakakin yace sun kwato shanun sata 341 da makamai kala-kala guda 41 da suka hada da bindigogi da adduna da dai makamantansu. An kai barayin kotu masu shanu kuma an mayar masu da dukiyarsu.

Akasarin shanun satan an satosu ne daga jihohin Zamfara da Kaduna da kuma wasu jihohi dake makwaftaka da jihar Neja.

Shugabannin Fulani sun tabbatar da cewa an mayarda shanun ga masu su. Alhaji Usaini Boso mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah yace duk wanda ya zo yace shanu nashi ne an bashi. Yaro daya ne ba'a bashi ba wanda yace uwarsa ce ta bashi shanu 30 sai suka ce ya tafi ya kawo uwar tasa.

Shugaban rikon kugiyar Miyetti Allah a jihar Neja Alhaji Adamu Kaduna yace koda mutanen sun nuna shanunsu sai sun sha rantsuwa kafin a basu.

A wani halin kuma rundunar 'yansandan ta Neja tace ta cafke wasu mutane shida da suka kware wajen sace mutane suna garkuwa dasu domin neman kudin fansa. Mutane biyar da aka sace duk 'yansandan sun kwatosu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Jihar Neja 'Yansanda Sun Kwato Shanun Sata - 2' 46"