Matsalar sace sacen shanu na cikin matsalolin tsaro da ake fama dasu a jihar Taraba da wasu sassan Najeriya.
A jihar Taraba kawai sama da makiyaya 164 suka rasa rayukansu a hannun masu satar shanu. A tsakanin shekarar 2013 zuwa yau an sace shanu kimanin 17,000 a jihar.
Matsalar ta sa dubban makiyaya barin jihar Taraba zuwa wasu jihohin. Dalili kenan da kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen jihar Taraba ta yi kira mahukunta su dauki matakin dakile matsalar.
Alhaji Mafindi Dan Buram shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Taraba yace lamarin ya fi kamari ne a kananan hukumomin Gasol, Takum, Ibi, Bali Donga da Wukari. Sun kara da zargin kabilar Jukun da kora masu shanu fiye da dari daya cikin kwanakin nan.
Amma hadakar al'ummar Jukun ta bakin shugabanta Mr. Benjamen Bako ta musanta zargin cewa suke sacewa Fulani shanu. Yace barayin shanu suna koina a arewacin Najeriya. Yace a wani bincike da aka yi su Fulanin suna da hannu a satar shanu.
A nata martanin rundunar 'yansandan Najeriya tace tana sane da matsalar kodayake kawo yanzu babu wanda aka kama. Kakakin 'yansandan DSP Joseph Kwaji yace suna nan suna sintiri kuma suna kiran Fulani duk lokacin da aka yi masu barna su kira 'yansanda domin a dauki mataki.
Ga karin bayani.