A jihar Neja Kungiyar Kristoci Ta Yaba Da Matakan Da Ake Dauka Ta Fuskar Tsaro

Kungiyar Kristocin Najeriya reshen jihar Neja tace ta gamsu da irin ci gaban da ake samu a wannan gwamnati, ta fuskar tsaro da yankin Arewacin Najeriya.

Shugaban kungiyar Kristocin a jihar Reverend Matthias Eciyoda, yace ya zuwa yanzu sun gamsu akan matakin da aka dauka. Shugaban Kristocin dai yayi magana ne jim kadan bayan da gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da shi a matsayin shugaban wani kwamitin mutane 16, da zai yi aikin wayar da kan mabiya addinin Krista muhimmancin zaman lafiya a jihar.

Babban darakta a ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar Neja, Sheikh Umar Faruk Abdullahi, yace sun fadakar da kwamitin cewa ayi gaskiya da rikon amana, haka kuma a guji gina Majami’u a kusa da juna musamman ma idan akwai banbanci na akida.

Shguaban agajin kungiyar Izala a Najeriya, Injiniya Mustapha Imam, yace samar da irin wadannan kwamitoci na da amfani matuka, domin zai wayar da mutane kai wajen sanin aikin tabbatar da tsaro bana gwamnati bane kadai na kowa da kowa ne,

Masana harkokin tsaro na bayyana cewa samar da irin wadannan kwamitoci a matakin kasa yana da tasiri wajen inganta tsaro.

Saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

A jihar Neja Kungiyar Kristoci Ta Yaba Da Matakan Da Ake Dauka Ta Fuskar Tsaro - 2'33"