Tun farko ministar kudin Najeriya Femi Adeosun tace ya zama wajibi kasar ta nemo lamunin kudi daga ketare domin raya tattalin arziki saboda Najeriya bata da wani zabi.
Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara shi ya karanta bukatar da shugaban kasa ya gabatar masu.
Bayanan dake kunshe cikin wasikar ta shugaban kasa sun nuna za'a yi anfani da kudaden ne wajen cike gibi a bangaren kiwon lafiya, ilimi, samarda ruwan sha da dai sauransu.
Cikin kudin kasafi kuma akwai ayyukan kafa cibiyoyin samarda watar lantarki a Gwaram da Gagarawa dake jihar jjigawa.
Karbo lamunin don cike gibin kasafin kudi ya fi alheri akan sayarda kadarorin gwamnati masu mahimmancin don samun kudin, inji mukaddashin shugaban bunkasa hanyoyin tara kudaden shiga da raba arzikin kasa, Shettima Abba Gana.
Gara a ciwo bashi idan an biya bashin kuma kadarorin zasu zauna a hannun kasar kuma darajarsu zata karu inji Shettima Abba Gana tare da cewa shawarar da suka bayar ke nan. Yace wannene ya fi sauki? A ciwo bashi a ga kadarorin da za'a yi dasu ko a sayar da kadarorin? Duk kadarorin da aka sayar ba zasu sake dawowa ba, inji Gana.
A cewar Shettima Abba Gana "Muna cikin gwamnatin shugaba Buhari ba zamu ji tsoron ya ciwo bashi ba domin ba sacewa zai yi ba" Ya kara da cewa da ace gwamnati ce mai sata da sai mu ji tsoro amma shi aiki zai yi da gaskiya, inji Gana.
Ga masanin tattalin arziki a Abuja Abubakar Ali akwai bukatar tallafawa kananan masana'antu a lamunin da za'a karbo don haka zai sa su shaida muradun gwamnatin. Ya bada yadda za'a bunkasa kananan masana'antu su rika kawo riba.
Inji Abubakar Ali a duba abubuwan da za'a fara sarafawa nan take. Babu bukatar IMF yanzu. Shugaban kasa ya shirya kasuwar baza koli a kawo takalma daga kofar mata dake Kano, a kuma kawo daga Aba kana shugaban kasa ya bada odar sayan 12 ya kuma ce daga yau ya daina sa takalman kasashen waje, inji Ali. Da zara ya yi hakan kasuwar masu takalman Kano da Aba zata tashi.
Abubakar Ali ya cigaba da cewa "duk ministocin Buhari da gwamnoni su fara sayen kayan cikin gida suna sawa. Idan hakan ya faru kowa ma zai fara kwaikwayonsu.
Ali yace idan 'yan Najeriya basu canza halayensu ba kasar ba zata fita daga tabarbarewar tattalin arziki ba. Ya kamata a daina zuwa asibitocin kasahen waje da daina sayen motocin waje da daina kai yara karatu kasashen waje idan ana son kasar ta cigaba.
Amma hukumar bada lamuni ta duniya tace tattalin arzikin Najeriya ya farfado fiye da kowace kasa a Afirka.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.