Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Sun Kara Fahimtar Salon Mulkin Buhari


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Kama daga kukan kuncin tattalin arziki zuwa ga rashin bada mukamai ga wadanda suke ganin sun yiwa jam'iyyar Buhari hidima bayan kimanin shekara daya da rabi, yanzu an kara fahimtar salon mulkin Buharin

Tun kafin ya kafa gwamnati Shugaba Buhari yace zai sa mukaman gwamnati su zama ba abun rububin nema ba ne.

Wani dan APC Nasiru Marmara yace duk wanda ya zabi Buhari domin neman mukami ya tafka kure. Yace shi bai taba jin wani yace Buhari bashi da gaskiya ba wanda kuma shi ne abu mafi mahimmanci da ake so da shugaba. Maganar bada mukami ba sai ya san mutun ba, muddin mutumin nada cancanta. Wasu ma da ya basu bai sansu ba. Ya bi tarihinsu da zamantakewarsu kafin ya basu aiki.

Ministan wasanni da matasa Solomon Dalung yace nan gaba kadan za'a soma samun ribar gwamnatin da suka hada da inganta tsaro da hana almundahana. Yace yanzu ba'a kashe kudin gwamnati akan buki. Ba'a kashe kudin gwamnati akan yawon banza. Ba'a kashe kudin gwamnati akan sayen takardun bogi.

Solomon Dalung yace matakan da aka dauka suna da zafi amma zasu haifi da mai ido. Yace akwai wadanda suke neman su kifar da mulkin Buhari ko su bata shi. Wasunsu suna boye shinkafa domin mutane su sha wuya, a yi yunwa mutane su ga bakin shugaba.Wasu ma gonaki suke bi su saye albarkatun gona duk da zummar kawo cikas.

Ga rahoton Sale Shehu Ashaka da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG