Kakakin rundunar tsaron Keften Ikedichi Iweha ya shaidawa Muryar Amurka cewa suna rike da barayin shanun da masu sayen shanun sata da masu yanka shanun suna sayarwa.
Yace da suka samu rahoton barayin sai suka fara bincike har suka kama mutane shida. Yawancin kwantan baunan da ake yi barayi ne suke aiwatarwa. Yace suka soma kamawa suna ta yin haka har cikin garin Bukuru suka samesu. Yace inda basu dauki matakan zakulo barayin ba da yanzu an rasa rayuka
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Filato Alhaji Nura Abdullahi ya yabawa jami'an tsaron bisa ga kokarin da suka yi har suka kamo barayin. Amma yace har yanzu dai akwai sauran aiki. Yace suna iyakacin kokarinsu domin su tabbatar zaman lafiya ya dawo jihar. Suna zagayawa suna jawo hankalin jama'arsu domin a zauna lafiya.
Sanadiyar hadin kan da suka samu daga jami'an tsaro, Alhaji Abdullahi yace, shanun da ka sace tun daga watan biyu zuwa yanzu wajen garkuna 22, tare da kashe mutum uku, an dawo da garkuna 18.
Shi ma shugaban kungiyar matasan Berom na kasa Chogi Dalyop yace duk da kwarya kwaryar zaman lafiya da aka samu har yanzu ana fuskantar kisan sari ka noke a wasu yankunan. Yace yanzu da damuna ta sauka mutanensu sun fara aikin gona sai dai wasu Fulani suna kiwo har su shiga gonaki lamarin da kan kaiga tashin hankali.
Rahotanni daga yankunan iyakokin Filato da Taraba na nuna an samu hasarar ran mutum guda yayinda a yankunan kananan hukumomin Wase da Langtan ta Arewa ake samun rashin jituwa kan filin noma inda al'ummomin yankin ke bukatan jami'an tsaro su kara sa ido.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5