A Jamhuriyar Domokaradiyar Congo An Gano Moise Katumbi Laifin Amfani Sojojin Haya

FILE - Moise Katumbi Chapwe

Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta kaddamar da bincike game da zargin da ake ma fitaccen dan adawar siyasa Moise Katumbi, na amfani da sojojin haya na kasar waje, a cewar jami'an gwamnati jiya Laraba.

Ministan Shari'a Alexis Thamba, ya ce gwamnati ta tattara hujjojin da ke nuna cewa wasu tsoffin sojojin Amurka da dama na aiki ma Katumbi a lardin Katanga a matsayin dogarawan tsaro.

Katumbi, wanda ya taba zama gwamnan yankin Katanga mai arzikin ma'adanai, ya fice daga gwamnatin Joseph Kabila a watan Satumba ya koma bangaren 'yan adawa.

Ranar Lahadin da ta gabata, wata kungiyar 'yan adawa ta bukaci Katumbi da ya tsaya takara a zaben Shugaban kasar da za a yi wannan shekarar. Jiya Laraba Katumbi ya yi na'am da wannan bukatar.

Ya karyata zargin cewa ya na tara sojojin haya, ya ce manufar zargin shi ne a kassara shi a siyasance.

To amma Ministan Yada Labarai Lambert Mende ya ce ana samar da sojojin hayar ne ta wajen amfani da wani kamfanin da ke jahar Virginia ta Amurka. "An damke wasu mutane a Lubumbashi kwanan nan, yayin da su ke wani yinkuri na tayar da zaune tsaye bisa tituna tare da Mr. Katumbi ranar 21 ga watan Afirilu, kuma bayan da su ka bincike asalinsu, sai aka tarar da wani ba-Amurke mai ikirarin cewa shi wani kwararre ne a fannin noma," a cewarsa.