A Cimma Daidaito Kan Kasafin Kudin Amurka

Majalisar Dokokin Amurka.

Shugabannin majalisar Dattijai da ta wakilan Amurka sun ce sun cimma daidaito kan kudaden gudanar da gwamnati da zai kauda barazanar tsaida harkokin gwmanati baki daya.

Shugabannin majalisar Dattijai da ta wakilan Amurka sun ce sun cimma daidaito kan kudaden gudanar da gwamnati da zai kauda barazanar tsaida harkokin gwmanati baki daya.

Da misalin tsakar ranar Jumma’an nan ce wakilan majalisar dokokinAmurka suka kada kuri’a kan kudurin kasafin kudi wadda ya samar da kudaden gudanar da gwamnati daga yanzu zuwa watan oktoban badi. Wakilai 296 suka goyi bayan kudurin, yayinda wakilai 121 suka ki.

Kakakin majalisar wakilai John Boehner, ya fada a safiyar Jumma a cewa kudurin ya sami goyon bayan wakilai daga manyan jam’iyun biyu.

Tsohuwar kakakin majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi,wacce ita ce shugabar marasa rinjaye a majalisar wakilai, ta zargi ‘yan Republican da janyo jinkiri da aka samu, sabo da siyasa kawai.

Aika Sharhinka