A Al’adance Ana Tura Tubabben Sarki Zaman Hijira - Barayan Bauchi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II

A yayin da masana kimiyyar siyasa, da na shari’a, da kuma mutanen gari ke ci gaba da muhawara kan al’adar tura sarkin yanka da aka sauke zaman hijira a nesa da masarautar sa, Ya’u Kacha, Sarkin Bindigar Sarkin Daura ya ce tura tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II zama hijira a jihar Nasarawa a al’adance ba laifi ba ne.

Sarakuna a tsohuwar Daular Sokoto ta Shehu Usman Dan fodio na samun damar mulki har karshen rayuwar su, ko kuma su rasa mulkin don sabani da jagororin larduna na turawa, gwamnonin farar hula da kuma na mulkin soja kamar yadda ya faru a zamanin marigayi Janar Sani Abacha, lokacin da aka sauke Sultan Ibrahim Dasuki daga sarauta.

Ahamd Ibrahim Lau, Masanin tarihi da siyasa ne ya ce, ba sabon abu ba ne tsige Sarki sannan a tura shi zaman hijira a tsohuwar Daular.

Barista Yusuf Sallau Mutum biyu, Lauya ne mai zaman kan sa a Abuja, ya ce tura sarkin da a ka sauke zaman hijira ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Shi ma Sunusi Baban Tanko, Barayan Bauchi, yana mai ra'ayin cewa a al'adance ba laifi ba ne a tura sarkin yanka zaman hijira. Ya kuma ce an dade ana bin wannan al'adar don gudun tarzoma a masarautun gargajiya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

A Al’adance Ana Tura Tubabben Sarki Zaman Hijira: Barayan Bauchi