Mallam Umar Dahiru, Masanin tarihin tsarin sarauta a Kano ya ce, tsarin sauya matsugunni ga sarakunan gargajiya bayan da suka yi marabus ko aka sauke su daga kan karaga, ba sabon abu bane, ya kara da cewa, turawan mulkin mallaka ne suka shigo da wannan tsarin.
Muhammadu Sanusi na biyu shine sarki na biyu da aka saukewa a jerin sarakunan Fulani na Kano, yayin da kakansa Sir Muhammadu Sanusi ya zama Sarki na farko da aka sauke a masarautar.
Dr. Nasiru Adamu Aliyu, masanin harkokin shari’a dake tsangayar Nazarin aikin lauya ta jami’ar Bayero a Kano, ya ce, dokoki kare hakkin dan Adam ta Afrika ta kare al’ada da gargajiya.
Dr. Nasiru Adamu Aliyu ya kara da cewa kotu za ta iya warware irin wannan takaddama.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum