Dubban Mata ne suka gudanar da zanga-zanga a titunan biranen kasar Turkiyya, domin tunawa da ranar mata ta duniya, inda suka nuna adawa da rashin daidaito da cin zarafin Mata.
WASHINGTON D.C. —
A bangaren Asiya na Istanbul, Mata sun saurari jawabai, raye-raye da rera waka a lokacin bazara, yayin da dimbin 'yan sanda ke kula da su.
Jama'a a Diyarbakir, birni mafi girma a kudu maso gabashin Turkiyya da ke da rinjayen Kurdawa, sun gudanar da bukukuwan samun zaman lafiya da yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan Kurdawa suka sanar a makon jiya.
Masu suka dai na zargin gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan da sanya ido kan takunkumin da aka yi wa Mata da kuma rashin yin abin da ya dace wajen magance cin zarafin Mata.