NLC Ta Bada Shawarar Karin Kaso 5 Cikin 100 Kan Kudin Kiran Waya

Zanga-zangar NLC

Ya kuma ce babu gudu ba ja da baya kan batun zanga0zangar gama-garin da aka shirya gudanarwa a ranar Talata 4 ga watan Febrairu mai kamawa, domin nuna rashin jin dadin kungiyar da sanarwar karin kudin kiran wayar da sayen data na baya-bayan nan.

Kungiyar kwadagon Najeriya (nlc) ta caccaki gwamnatin tarayyar kasar game da aiwatar da manufofin bankin duniya da asusun bada lamuni na duniya (imf) da ake yiwa lakabi da Bretton Woods Intitutions, inda tace janye tallafin man fetur da karin haraji na kassara ‘yan najeriya.

“Suna cigaba da kassaramu ta hanyar wawayen haraji. za’a kai gabar da mutane na iya biya amma ba zasu biya din ba,” kamar yadda mai magana da yawun kungiyar nlc Benson Upah ya bayyana a shirin tashar talabijin ta Channels na hantsi mai suna “Sunrise Daily” na yau Alhamis.

Jami’in kungiyar kwadagon yayi fatali da sanarwar baya-bayan nan ta karin kudin kiran waya da kaso 50 cikin 100 da hukumar kula da kamfanonin sadarwa a Najeriya (ncc) tayi, tare da yin tayin karin kudin kiran waya da sayen data da kaso 5 cikin 100.