Kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta bayyana cewar zata kaddamar da wani gangamin gama-gari a ranar Talata 4 ga watan Febrairu mai kamawa, domin nuna adawa da karin kaso 50 cikin akan kudin kiran waya da sayen data da hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da shi a baya-bayan nan.
A cewar sanarwar bayan taron da shugaban NLC, Joe Ajearo ya sanyawa hannu a yau Laraba, an yanke shawarar ne yayin wani taron gaggawa da kwamitin gudanar kungiyar na kasa ya kira a yau Laraba.
A cewar NLC, gangamin zai kasance gargadi kan hatsarin dake tattare da rashin dacewar karin akan al'umnar dake karbar mafi karancin albashi na ₦70, 000 da mummunan karin a farashin man fetur da kayan abinci da lantarki da hauhawar farashin kayan masarufi.
A baya-bayan nan, kungiyar ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na karin kudin kiran waya da kashi 50 cikin 100.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Laraba dauke da sa hannun Shugabanta Joe Ajaero, NLC ta ce matakin zai kara ta’azzara halin tsadar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki.
“Wannan karin kudi na nuni da cewa gwamnatin ta fi fifita ribar da kamfanoni ke samu sama da bukatun ‘yan kasarta.
“NLC ba ta adawa da yin garanbawul ga haraji, amma ba ta amince da girman karin da aka yi ba.” Sanarwar ta ce.
Kungiyar ta kara da yin kira ga ‘yan Najer
Dandalin Mu Tattauna