Majalisa Ta Tabbatar Da Marco Rubio A Matsayin Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Marco Rubio

A kuri'ar da aka kada, Marco Rubio ya samu amincewar duk ‘yan majalisar, wanda ya tabbatar wa Trump mutum na farko daga cikin wadanda za su taya shi aiki.

Sanatoci sun ci gaba da aiki a majalisa a daren jiya Litinin bayan da aka rantsar da Trump. Rubio ya kasance wanda ba shi da matsala cikin wadanda Trump ya zaba da za su yi aiki tare da shi.

Ana sa rai cewa za a dau matakan tantance wadanda Trump ya zaba su yi aiki tare da shi cikin makon nan, wanda ya hada da wanda yake so ya nada a matsayin sakataren tsaro, tsohon mai sharhi kan harkokin tsaro a kafar labarai ta Fox News, Pete Hegseth.

Ba abin mamaki ba ne majalisar dattijai ta tabbatar da wasu da shugaban Amurkan ya mika sunansu a matsayin wadanda za su yi ai tare da shi a ranar da aka rantsar da shugaban kasa.