An ayyana jiya Alhamis a matsayin Ranar Makoki ta Kasa baki daya a Amurka, saboda rasuwar tsohon Shugaban kasa Jimmy Carter, ta yadda cibiyoyin gwamnati da dama su ka kasance a rufe, wasu harkokin kuma aka jinkirta su. Manyan jami’an gwamnati sun taru a babbar Majami’ar kasa da ke birnin Washington DC, saboda hidimar jana'iza ta kasa ga shugaban kasa na 39 din.
Carter, wanda ya mutu a makon jiya ya na mai shekaru 100 a duniya, a matsayin tsohon shugaban kasa mafi tsufa, ya yi watsi da wasu ka’idojin siyasa da gwamnati mai mazauni a Washington kan bi. To amma dukkannin shugabanni biyar da su ka zo bayansa da ke raye - wato Bill Clinton, da George Bush, da Barack Obama, da Donald Trump, da Joe Biden – duk sun halarci hidimar shirye shiryen jana’izarsa, inda Biden ya jinjina ma sa da cewa:
“Na koyi darasi daga abota irin ta Jimmy Carter – kuma ya koyar da ni ta wajen tsarin rayuwarsa -- cewa halin kirki ya fi duk wani matsayi ko ikon da mu ke da shi tasiri. Martaba ke sa a iya gane cewa ya kamata a dauki kowa da mutunci da kuma girmamawa. Don haka kowa, kuma ina nufin kowa, ya cancanci adalcin samun dama, ba wai tabbacin hakan kawai ba, dama dai da ta dace”.