Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Jimmy Carter Jana’izar Kasa A Birnin Washington DC


Shugaban Biden yana karrama Jimmy Carter lokacin jana’izarsa
Shugaban Biden yana karrama Jimmy Carter lokacin jana’izarsa

Bayan kammala taron addu’o’i a babban cocin kasar, za a mayar da gawar Carter zuwa mahaifarsa ta Plains, dan karamin garin da ya fara tare da kare rayuwarsa ta shekaru 100

Kwanaki 6 na yin ban kwana da gawar Jimmy Carter sun kare a yau Alhamis inda shugaban Amurka na 39 ya samu jana’izar ban girma a babban majami’ar kasar gabanin mayar da gawar tasa zuwa mahaifarsa ta Plains da ke Georgia, domin birnewa a gefen matarsa, Rosalynn.

Taron addu’o’in ya kawo karshen bajen kolin gawarsa a Majalisar Dokokin kasar, inda a jiya Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta jagoranci bikin bayyana yabo ga mamacin.

Shugabannin Amurka 5 da ke raye ne suka halarci jerin gwanon rakiyar gawar shugaban Amurka mafi dadewa a raye, cikinsu kuwa harda zababben shugaban kasa Donald Trump.

Bayan kammala taron addu’o’i a babban cocin kasar, za a mayar da gawar Carter zuwa mahaifarsa ta Plains, dan karamin garin da ya fara tare da kare rayuwarsa ta shekaru 100.

Jikan Jimmy Carter, Jason Carter ya yi jawabi akan kakansa lokacin jana’iza a Washington National Cathedral idake Washington, Jan. 9, 2025.
Jikan Jimmy Carter, Jason Carter ya yi jawabi akan kakansa lokacin jana’iza a Washington National Cathedral idake Washington, Jan. 9, 2025.

Za a gudanar da wata kebabbiyar jana’izar a majami’ar Baptist ta Maranatha, inda ya koyar a makarantar Lahadi bayan da shekarunsa sun zarta 90, gabanin a birne shi a gefen mai dakinsa Rosalynn, da suka shafe shekaru 77 a tare.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG