Firai Ministan Kanada Justin Trudeau Ya Yi Murabus

Za a dorawa sabon shugaban jam’iyyar Liberal din alhakin nema mata karin goyon baya gabanin babban zaben kasar da wajibi a gudanar da shi a cikin shekarar da muke ciki.

Firai Ministan Kanada Justin Trudeau ya sauka daga kan mukaminsa.

Firai Ministan ya sanar da murabus din nasa ne yayin wani taron manema labarai a yau Litinin.

Trudeau, wanda ke fuskantar rikicin siyasa mafi muni tun bayan zamowarsa Firai Minista a 2015, ya sanar da cewa zai sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar Liberal mai mulkin kasar, amma zai rike mukamin firai ministan riko kafin jam’iyyar ta zabi sabon shugaba, matakin da ka iya daukar tsawon watanni.

Za a dorawa sabon shugaban jam’iyyar Liberal din alhakin nema mata karin goyon baya gabanin babban zaben kasar da wajibi a gudanar da shi a cikin shekarar da muke ciki.

AFP