Yadda Za A Magance Yin Cushe A Kasafin Kudi - Shehu Sani

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.

Sanata Shehu Sani ya bayyana daya daga cikin hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalar yin cushe cikin kasafin kudin da hukumomi da ma’aikatun gwamnati suka gabatar.

A sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na X a yau Talata, Shehu Sani yace, “hanya daya tilo ta magance yin cushe cikin kasafin kudi ita ce yin dokar da zata haramtawa ‘yan majalisa sauya fasalin kasafin kudin da hukumomi da ma’aikatun gwamnati suka gabatar musu,” kamar yadda wani bangare na sakon tuwitar da sanatan ya wallafa ke cewa.

Sanata Shehu Sani

Sai dai, nan take ya kara da cewa, yana shakkar ko ‘yan majalisar zasu amince su yi dokar da za ta dakatar da hakan, ko kuma za’a bari irin wannan kudiri ya wuce a majalisar.

“Sai dai ba san wanda zai yi wannan dokar ba ko kuma yadda za ta tsallake karatun farko,” ya kara da cewa.

Shawarar tasa na zuwa a dai dai lokacin da taron kwamitin kasafi da ministan kudi da tattalin arziki da ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki da babban daraktan ofishin kasafi na tarayya ke daf da kankama a ranar Talata 7 ga watan Janairun 2025.

Haka kuma an tsara bayyanar hukumomi da ma’aikatun gwamnati domin kare kasafin kudinsu a gaban kananan kwamitocin kasafi tsakanin ranar Laraba 8 zuwa Laraba 15 ga watan Janairun 2025.

Ku Duba Wannan Ma Shugaba Tinubu Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekara Ta 2025