DANDALIN ‘YAN JARIDA: Tattaunawa Kan Tankiyar Diflomasiyya Tsakanin Nijar da Najeriya, Disamba 29, 2024

Souley Mummuni Barma

A wannan makon shirin ya tattauna kan tankiyar diflomasiyar da ta barke a tsakanin Najeriya da Nijar inda Shugaban Nijar ya zargi shugaban Najeriya da karbar kudade don bai wa Faransa damar kafa sansanin sojojinta a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Haka kuma za a ji matsayin ECOWAS akan wannan al'amari da ke zuwa a wani lokacin da kungiyar ke laluben hanyoyin bikon Nijar da Mali da Burkina Faso bayan da suka fice daga sahun mambobinta.

Bakinmu sun hada da Amma Moussa na Anfani FM Zinder da jaridar l'Eclosion sai Ibrahim Moussa babban editan jaridar La Roue de l'Histoire Info.

A yi sauraro lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

DANDALIN ‘YAN JARIDA: Tattaunawa Kan Tankiyar Diflomasiyya Tsakanin Nijar da Najeriya, DISAMBA 29, 2024.mp3