Zababben Shugaban Amurka Donald Trump Ya Zabi Mark Burnett A Matsayin Manzon Amurka A Birtaniya

Donald Trump tare da Mark Burnett

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da zabar Mark Burnett wani dakare da ya taimaka wajen sake gabatar da Trump din ga wani Shirin talbijin da yan kasa suka kalla mai suna ‘’ The Apprentice’’ a matsayin manzon Amurka a Birtaniya a sabuwar gwamnatin sa da ke tafe.

Mark wanda kwararre ne kuma shahararre a shirye shiryen Talbijin da fagen kasuwanci, ya hada da nasibi a harkar diplomasiyya, da ya ja hankalin duniya a muhimmiyar rawar da ya rika takawa, kamar yadda Trump ya bayyana a ranar Asabar.

Burnett wanda haihuwar Landan ne, ya taimaka wajen samar da shirye shirye irin su ‘Survivor da The Voice’’, to amma da alama an fi sanin shi a shirin ‘The Apprentice’’ bayan da ya kulle da Trump da aka fara dorawa a kafar NBC a shekarar 2004.

Trump yayi suna sosai a harkar saye da sayar da gidaje, da sauran al’amurra da suka shafi al’umma na tsawon gwamman shekaru. Shirin yasa Trump yayi suna ya zama hantsi leka gidan kowa. Trump ya raba gari da NBC a shekarar 2015, daidai lokacin da ya kaddamar da nema shiga fadar white House a karon farko.

Zaben na Burnett cigaba ne da cike guraben mukaman ga mutane muhimmai masu alaka da aikin talbijin ko siyasa, ko kuma duk biyun, da za su yi aiki a gwamnatin sa, da ya hada da zabin shin a sakataren tsaro Pete Hegseth, tsohon mai magabatar da Shirin ‘Fox& Friends na karshen mako, da wani shima da ya taba takarar sanata a Pennsylvania bai yi nasara ba, Mehmet Oz.

Yakin neman zaben Trump na farko a shekarar 2016 ya yi fama da zarge zarge game da halayyar sa a cikin Shirin ‘The Apprentice’ da fitowar da ya rika yi a kafar NBC, musamman a inda yace, zai iya cin zarafin mata ta hanyar lalata kuma ya ci nanin, saboda shaharar shi.

Kusan shekara goma bayan barin irin rawar da ya rika takawa a Shirin talbijin din, duk da haka aikin da Trump yayi na talbijin na nan daram a tarihin daukakar shi a siyasa. Shirin ya rika haska ginin shin a Trump Tower ga milyoyin mutane a matsayin wani tambarin karfin shi da nasarorin shi tun kafin ya kaddamar da kampe din shin a farko da ga farfajiyar ginin.