Hukumar Zaben Ghana ta ayyana tsohon shugaban kasar John Mahama a mastsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Shugabar hukumar zabe ta Ghana, Jean Mensa, ta ce kashi 60.9 cikin 100 na mutum fiye da miliyan 18 ne da ke da rajista suka fita kada kuri'ar.
“Ina ayyana shugaban kasa John Dramani Mahama wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2024 kuma zababben shugaban kasa.
“Mr John Dramani Mahama ya samu kuru’u miliyan 6,328,397, wanda ya yi dai dai da kashi 56.55 cikin dari. Yayin da Bawumia na NPP ya samu kuru’u miliyan 4.657.304, wanda ya yi dai dai da kashi 41.67 cikin dari", a cewar Mensah da misalin karfe 5 da rabi na yau Litinin
Sai dai ta bayyana sakamakon ne ba tare da sakamako daga mazabu 9 ba, wanda suke da kuru’u kusan dubu 900, amma lissafi ya nuna ba zasu iya sauya nasarar da John Mahama ya yi ba.
“Da a ce dukkan mutane mazabu taran sun jefa wa mutumin da ya zo na biyu kuri’unsu, da zai samu kuri’u miliyan 5.604.420 wanda zai yi dai dai da kashi 46.17 cikin dari.”
Duk da cewar ba a bayyana sakamakon mazabu tara ba, NDC ta samu rinjayi da kujeru 165 cikin kujeru 276 na Majalisar dokokin kasar.
A ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2025 ne za a rantsar da zababben shugaban kasa John Dramani Mahama da ‘yan Majalisar dokoki 276 da za su yi aiki a sabuwar majalisa.
Ku Duba Wannan Ma Mahamudu Bawumia Ya Amince Da Shan Kaye A Zaben Shugaban Kasar GhanaA Ranar Lahadi dantakarar jam’iyar New Patriotic Party mai mulki a Ghana, mataimakin shugaban kasa Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasar.