Zulum Ya Kaddamar Da Aikin Jirgin Kasan Cikin Birni A Borno

Layin jirgin kasa a jihar Legas

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, na daf da fara aikin gina layin jirgin kasan da zai karade birnin Maiduguri da kewayensa.

Wannan aiki shine irinsa na farko da wata daga cikin gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya 19 ta kaddamar.

Kashin farko na aikin zai fara ne da gina tashoshin jirgin kasa 12 a kwaryar birnin Maiduguri, da zai karade manyan kasuwanni da makarantu da wuraren taruwar jama’a dana harkokin tattalin arziki.

Aikin, wanda za a iya fadada shi ya kai yankunan kananan hukumomi anan gaba, zai taimaka wajen saukaka jigilar fasinjoji da kayayyaki, tare da buda hada-hadar tattalin arziki da yankunan dake loko a fadin jihar.

Da yake rangadin duba tashoshi da hanyoyin farko da aka tsara na aikin jirgin kasa tare da kamfanin gine-ginen EEC da zai taimaka wajen gudanar da aikin, kwamishinan ayyuka na jihar Borno, Aliyu Muhammad Bamanga, yace ana aikin nazarin wuraren da aikin zai bi da auna illolin da aikin ka iya yiwa muhalli tare da tuntubar al’ummomin da aikin zai ratsa ta yankunansu domin tabbatar da nasarar aiwatar da shi.