ABUJA, NIGERIA - Bikin kaddamarwar da ya gudana ranar Laraba wanda ya samu halartar manyan jami'ain gwamnati da suka hada da mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, alkalin alkalan tarayya, da sauran manyan baki.
A nasa jawabin, shugaba Tinubu ya bayyana matukar alfahari da godiya bisa ganin yadda aka samu nasarar gudanar da wannan aiki, inda ya bayyana hakan a matsayin shaida na sadaukar da kai da hangen nesa na gwamnatin sa.
Shugaban ya tunatar da cewa, layin dogo na Abuja wanda aka fara aikin tun shekarar 2018 na gwamnatin baya da ya gada, ya fuskanci koma baya sakamakon annobar COVID-19 da kuma yin watsi da tasgaro da aikin ya rinka fuskanta.
Shugaban ya bayyana amincewar sa da muhimmiyar rawar da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya taka, inda ya yabawa tawagarsa bisa jajircewa da aiwatar da aikin da suka yi.
Shugaban ya jaddada cewa babu shakka ministan yayi abin a yaba masa kuma yana alfahari dashi ganin yanda nasarar aikin ya wuce tsammani tare da cika alkawarinsa na dawo da layin dogo na Abuja.
Da yake karkare jawabinsa, shugaban ya kuma yi kira da neman a tsawaita daukar jama’a kyauta maimkon tsawon watanni biyu a kaishi har karshen wannan shekara ta 2024.
Ministan babban birnin tarayya , Nyesom Wike a nashi jawabin, ya bayyana irin kokari da hadin kai da ya samu, wanda ya kawo nasarar aikin.
Wike ya bayyana abinda shugaban Najeriyan ya fada masa a baya na cewa yana so yaga ya hau dogon layin jirgin kasa na Abuja, wanda hakan ya bashi karfin gwiwa sosai wajen ganin an sami nasarar aikin.
Da yake karin haske kan abubuwan da suka gano, Wike yace sun gano cewa duk da cewa an kaddamar da layin dogon a shekarar 2017-2018, amma bai fara aiki ba saboda rashin hanyoyin shiga tashoshin jiragen kasa.
Wike ya yi karin bayani, "Yaya za ku gina tashoshin jirgin kasa ba tare da hanyoyin shiga ba?”
Gwamnatin ta sanya wa’adin watanni tara don aiwatar da aikin. Kwangilar gyaran layin dogo da aka fara bayar wa a shekarar 2018 kan kudi dala miliyan 30 ba a biya ba.
Ministan ya yaba da kokarin hadin gwiwa na Gwamnan Babban Bankin, Ministan Kudi, da Akanta Janar na Tarayya, wadanda suka taimaka wajen biyan kudin tare da tabbatar da ci gaba da aikin.
Har ila yau, Wike ya bayyana cewa aikin ya hada da gina hanyoyin shiga tashoshin jiragen kasa, wanda aka kashe Naira biliyan 21.4. An kammala waɗannan hanyoyi da wuraren ajiye motoci don tabbatar da aikin tashar jirgin a saukake.
Har ila yau, Ministan ya kuma yi magana game da tsadar kudaden da aka ware domin horar da ma'aikata. A bisa matsayar gwamnatin Buhari da ta shude, an amince da dala miliyan 128 don horar da ma’aikata, abin da ministan ya bayyana rashin amincewar su, tare da sake zama don samun daidaito.
Ta hanyar sake tattaunawa, an rage kudin zuwa dala miliyan 75, inda aka ceto dala miliyan 50.
Daya daga cikin mahalarta taron kuma malamin kimiyya a ma’aikatar ilimin tarayya, Malam Adamu Zaharaddin ya bayyanawa Muryar Amurka cewa babu shakka yayi farin cikin ganin yadda shugaban kasa yazo domin kaddamar da wannan tasha ta jirgin kasa wanda zata sauka tafiye tafiye a birnin na Abuja da ma kasa baki daya. Daga karshe Malamin yayi fatan sauran jihohi ma su bi sawu don inganta harkokin sufuri a kasa baki daya.
An kammala bikin ne inda shugaba Tinubu a hukumance ya ayyana layin dogon a bude domin fara gudanar da aikace aikace.
Za’a iya cewa layin dogo na Abuja ya kasance alama ce ta fara alƙawarin da gwamnatin ta yi na cika alkawuran da ta ɗauka na samar da tsarin sufuri na zamani da inganci ga mazauna Abuja. Ana sa ran dogon layin jirgin zai inganta hanyoyin sufuri na birnin da kuma inganta rayuwar mazauna birnin.
-Yusuf Aminu Yusuf
Dandalin Mu Tattauna