Kungiyar kwararrun likitoci da takwarorinsu na hakora (MDCAN) ta bayyana cewa a shekaru 5 din da suka gabata, mambobinta 1, 106 daga cikin 6, 137 ne suka yi kaura daga Najeriya zuwa wasu kasashen.
MDCAN ta kara da cewar mutum 1, 799 daga cikin mambobin nata, kwatankwacin kaso 29.31 cikin 100, na tsakanin shekaru 55 da haihuwa zuwa sama a yayin da kaso 1 bisa 3 na adadin ke shirin yin ritaya nan da shekaru 5 masu zuwa.
Shugaban kungiyar ta MDCAN, Farfesa Muhammad Aminu Muhammad, ya bayyana damuwar yayin wata ganawa da manema labarai a yau Talata.
Ya ci gaba da cewa, “binciken da aka gudanar a watan Janairun bana ya nuna cewa akwai kwararrun likitoci da likitocin hakora 6, 137 ne kacal a Najeriya, 3, 475 daga cikinsu na aiki ne a asibitoci yayin da 2, 668 ke zama kwararru a matakin girmamawa.
“Binciken ya kuma gano cewa kwararrun likitoci 1, 106 sun yi kaura zuwa wasu kasashe a cikin shekaru 5 da suka gabata kuma guda 1, 799 daga cikin 6, 137 (kaso 29.31 cikin 100) sun haura shekaru 55 da haihuwa. Hakan na nufin kusan kaso 1 bisa 3 na kwararrun likitocin da ake dasu a halin yanzu, duk da cewa adadin bai wadatar ba zasu yi ritaya nan da shekaru 5.
Hakan bai yi la’akari da dimbin kwararrun da za su bar aikin gwamnati saboda wasu dalilan da basu da nasaba da wadanda aka ambata a baya ba.