An saki likitar nan mai neman kwarewa a cibiyar kula da lafiyar idanu ta Najeriya dake jihar Kaduna, Ganiyat Papoola, wacce ‘yan bindiga suka sace a watan Disamban bara, bayan shafe watanni 10 a hannunsu.
An sace Dr. Papoola, wacce ta kasance magatakarda a fannin kula da lafiyar idanu na cibiyar, tare da mijinta, Nurudeen Papoola, wanda hafsan soja ne da dan danuwanta, Folaranmi Abdulmugni, dake zaune a wurinsu.
Tunda fari masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya tsabar kudi har naira milyan 40 a matsayin kudin fansa, wanda bayan biyansu suka saki mijinta a ranar 8 ga watan Maris din daya gabata, amma suka cigaba da garkuwa da Dr. Papoola da dan danuwanta.
Sai dai da yammacin jiya Laraba an sako Dr. Papoola da ‘yar dan uwanta, al’amarin daya kawo karshen mummunan zaman da suka yi a hannun wadanda suka yi garkuwa dasu.
Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya, Dr. Tope Osundara, ya bayyana matukar farin ciki da kwanciyar hankali da sakin Dr. Papoola, inda ya godewa dukkanin wadanda suka taimaka wajen kubutar dasu cikin aminci.
Dandalin Mu Tattauna