Ukraine ta harba makamai masu linzami kirar Amurka samfurin ATACMS zuwa cikin yankin Bryansk na kasar Rasha, a cewar ma’aikatar tsaron Rasha, a wata mummunar kazancewar rikici ana kwana na 1000 da fara yakin.
Harin na zuwa ne kwanaki 2 kacal bayan da gwamnatin Biden ta baiwa mahukuntan birnin Kyiv izinin yin amfani da makaman Amurka masu cin dogon zango a kan wurare a cikin Rasha.
Kyiv ba ta yi martani nan take a kan rahoton ba. Harin ya kasance karon farko da Ukraine ta yi amfani da makaman Amurka masu cin dogon zango a kan wuraren dake can cikin Rasha, kuma abin da ke alamanta cewa mahukuntan birnin Kyiv ba su bata lokaci wajen yin amfani da sabuwar damar da suka samu ba.
Ukraine ta harba makamai masu linzami 6 a kan wani gini a yankin Bryansk, a cewar ma’aikatar tsaron. Tace an yi amfani da makamai masu linzami kirar ATACMS wajen kai harin.
Rundunar tsaron samaniyar Rasha tace ta harbo 5 daga cikin makaman masu linzami tare da lallata guda.
Tarkacen makami mai linzamin da aka lallata sun tarwatse a harabar barikin sojin, abin da ya haddasa gobara da tuni aka kasheta. Babu asarar rai ko lalacewar wani abu a harin.
Ku Duba Wannan Ma Biden Ya Baiwa Ukraine Damar Yin Amfani Da Makaman Amurka Wajen Kai Hari Cikin RashaA Lahadin data gabata, Shugaban Amurka Joe Biden ya baiwa Ukraine izinin yin amfani da makaman Amurka masu cin dogon zango a cikin Rasha, abin da ya kawo karshen watannin da aka shafe ana haramta hakan da nufin baiwa Ukraine damar kare kanta ba tare da kara hura wutar rikicin ba.